ABNA24 : Jumillar wadanda su ka samu aka yi musu allurar sun kai dubu dari takwas da ashirin da hudu da dari daya da goma sha uku.
A gefe daya, mutanen da cutar ta corona ta kashe a cikin san’oi 24 da suka gabata a Iran sun kai 496, sai kuma wadanda su ka kamu da ita da suka kai 21,026.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ta sanar da cewa; Daga bullar cutar corona zuwa yanzu adadin wdanda su ka mutu a Iran sun kai 70,070.
342/